Ga ilimi kuma ga kyau
marar misaltuwa
Duguwa kuma ga fikira
Tanada hasken fata
Tanada kirki, da tattausar murya
Mai kwantar da hankali
Ga ado acikin shigarta
Kamar Yadda take sanye da abaya
Wannan itace
Batada tamka
Idan ai kaganta
Kawai kasan cewa
Zata sace zuciyarka
Kafin ka farga
Mas'uda ne sunana
Agareni Mai daraja ce
Bakamar ta
Kaduba ko'ina