Ba`kon Munafuki na kowane
In ka ganshi kamar ba kowa bane
Kalamunsa ba irin na kowa ba
Cike da soyayya da kulawa, kamar ba cuta zaiyi ba
Kamilin Mutum wani bi harda gemu
Ga Dadin zama don basu cewa bani
Dadin labari kamar Aku, don komai ya sani.
Sirrin kowa a tafin shi, har naka malam kasani
Abun mamaki kare da tallan tsire
Jiyo nan, fad'i cen, Mugun d'aya hada ya tsere
Gane munafuki da wuya. Kisan damo hankaline
Ko ina suna nan, Har Fada wollah
Gobara a kogi maganinta Allah.
This poem has not been translated into any other language yet.
I would like to translate this poem
Mutum! ! " Har naka malam kasani" . Thanks for sharing this poem with us.